14 Yuni 2021 - 09:35
Naftali Bennett, Ya Zama Sabon Firaministan Isra'ila

Majalisar wakilai a Isra'ila ta amince da sabuwar gwamnatin hadaka, wadda ta kawo karshen mulkin shekaru 12 na firaminista Benjamin Netanyahu.

ABNA24 : Gwamnatin ta kunshi jam'iyyun masu sassauci da tsattsauran ra'ayi da jam'iyyar Larabawa.

Karkashin yarjejeniyar raba madafun iko da aka cimma, hamshakin attaijiri kuma mai tsattsauran ra'ayi, Naftali Bennett, zai zama firaminista na shekara biyu kafin daga bisani ya mika ga Yair Lapid, mai ra'ayin sassauci.

Netanyahu, na fuskantar tuhume tuhume da suka hada da cin hanci da kuma karbar rashawa.

342/